ProZ aikin kyauta a kallo na hanzari
Mafi yawancin yanar gizo da turanci yake, amma muna so mu bawa abokan mu da abokan cinikin mu na kasashe na duniya dama don su san abun daya shafi wannan shirin da yarukansu. Wannan Shafin ya ƙunshe bincike game da aikin, mutanen da aikin ya shafa da kuma dalilin sa. An fassara shi ne daga fitattunmu masu aikin sa kai. Kuma a kula don Allah za ku iya rubuta mana da kowane yare kuma zamu dawo gare ku da irin Yaren ku.
Menene, waye, yaushe, A ina, Me ya sa?
Menene?
ProZ aikin kyauta shiri ne na sadaka kyauta ƙaddamarwar Proz.com, mafi girman al'umma masu fassara ƙwararru a duniya. Wanan shirin yana haɗa gwanaye wajen yare a kungiya mai zaman kanta tare da ɗaiɗaikun mutane masu buƙatar aikin fassara, duk a aikin sa kai yau da kullum. Daga wannan shirin na proz.com ne aka samu sauƙaƙe wa yarurruka na duniya ta cibiyar sadarwa da basu goyon baya, ta yadda zasu samu hanyar samun bayani da aiyuka ga jama'a da basa samun cikakken bayani.
Waye?
Shirin ProZ aikin kyauta yana hidima ga ƙungiyoyi masu zaman kansu a duk faɗin duniya, don su iya jawabi ga al'ummomin harsuna da yawa, da kuma sadaukar da ƙarancin albarkatun su ga babban burinsu na yi wa marasa galihu hidima. Shi fassara da fassarawa aiki ne na gwanayen wajen harsuna waɗanda suka yi rijista a matsayin mambobin proz.com. Waɗanan ɗaiɗaikun mutane suna so ga bada karfin gwiwa da tasiri wajen nuna gwanintar su a kyauta ga masu bukatar taimako. An biya ne daga mambobin proZ.com
A ina?
Shirin ProZ aikin kyauta yana aiki a duk faɗin duniya. Ƙwararrun masu fassara da ƙungiyoyi masu zaman kansu daga kowane lungu a cikin duniya za su iya shiga. Shirin yana yin amfani da yanayin kama-da-wane na ProZ.com, dabada damar haɗin gwiwar kan iyaka. Masu aikin sa kai na iya bayar da ayyukansu kuma masu cin gajiyar na iya buƙatar taimako ba tare da la’akari da wurin yankin da suke ba.
Yaushe?
Shirin proZ na kyauta yana kan tafiya tare da himma, kuma akwai yiyuwar sake halartarsa a shekara. Gwanaye kan yaruka na iya rijista a matsayin masu aikin sa kai a kowani lokaci, kuma ƙungiyoyi masu aiki badon riba ko daidaikun mutane da suke bukata zasu iya nema duk sanda ya zamo dole. Sauƙaƙawa a lokuta yana bada damar amsa nan-da-nan ga abin da ya danganci buƙatun yaruka.
Me yasa?
Shirin proZ na kyauta yana da amfani na musamman wajen haɗe tazarar ilimin harsuna ga waɗanda zasu iya ko fama don su samar ko su cin riba da muhimanci ta hanyar bada labari da kuma aiyuka. Yayi daidai da darajar cibiyar ProZ.com, waɗanda sune haɓaka haɗin gwiwa da goyan baya a cikin fassara da fassarawa ga jama a kuma da kawo canji mai ma'ana a duniya. Wannan shirin ya cike manufa mafi faɗi wajen haɓakar fahimta, sadarwa da kuma samun damar bayanai a duniyance.
Shirin nan yana tausayawa da kuma tasiri ga ƙoƙari wajen karfafawa gwanayen yaruka da yin amfani da ƙwarewarsu, wajen yin aikin sa kai, da kuma bada muhimman aiyuka ga waɗanda suke buƙata a duniya baki ɗaya. Masu aikin sa kai na fassara da fassarawa a cikin Shirin ProZ suna ba da gudummawar fasaharsu da ƙwarewar su, ba don amfanin kansu ba, sai don yin tasiri mai kyau ga rayuwar masu buƙatar tallafin harshe.
Yi duba ga shafin jakadu don dubawa ko kasarku ko harshenku nada nata jakadan.
Translated by/Fassara daga: Hussaina Aliko Maishanu & Shafiu Ahmad